Kano Pillars ta doke Gombe United da ci 2-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Sauran wasanni biyar a kammala gasar Premier Nigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Gombe United da ci 2-0 a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 33 da suka buga ranar Alhamis.

Pillars ta fara zura kwallo a ragar Gombe United a dukan fenariti da golan Pillars Joel Theophilus ya ci a minti na 29, kafin Moses Akpai ya kara ta biyu a minti na 51.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Nembe City ta zurawa Kaduna United kwallaye 4-0, hakama Taraba United ta zazzagawa Akwa United kwallaye 4-1.

Warri Wolves doke Lobi Stars tayi da ci 3-0, Elkanemi ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Dolphins a Fatakwal.

Ita kuwa Enyimba ta hada maki uku rigis bayan data doke Nasarawa United da ci 3-1, karawa tsakanin Giwa FC da Sharks ta Fatakwal tashi aka yi baran-baran.

Har yanzu Kano Pillars ce a matsayi na daya a teburi da maki 56, inda Warri Wolves ke mataki na biyu da maki 55 bayan buga wasannin mako na 33.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Abia Warriors 2-0 Bayelsa United - Dolphin 1-0 El-Kanemi Warriors - Enugu Rangers 1-0 Heartland - Enyimba FC 3-1 Nasarawa United - Kano Pillars 2-0 Gombe United - Nembe City FC 4-0 Kaduna United - Sunshine Stars 2-0 Crown FC - Taraba FC 4-1 Akwa United - Warri Wolves 3-0 Lobi Star