Amodu ya maye gurbin Keshi a Super Eagles

Shuiabu Amodu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyar da Amodu zai horas da Nigeria

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF ta maye gurbin Stephen Keshi da Shuaibu Amodu a matsayin kocin Nigeria.

NFF ta yanke hukuncin sauke Keshi daga matsayin kocin Super Eagles, bayan kammala taron da kwamitin amintattun NFF ya gudanar domin kamo bakin zaren matsalar kwallon kafar Nigeria.

Kwamitin ya dora wa Amodu alhakin kai Nigeria gasar cin kofin Afirka a karawar da za ta yi da Congo da kuma Sudan kafin a nada sabon koci dan kasar waje.

Haka kuma an yiwa Keshi tayin karo ilmin horas da kwallon kafa da shi da Amokachi da kuma Shorummu da za a biya musu kudin dawainiya a duk inda suka zaba.

Shuaibu Amodu wanda ya horas da Super Eagles har sau hudu, zai yi aiki ne tare da Salisu Yusuf da Gbenga Ogunbote da Aloysius Agu.

Haka kuma kwamitin amintattun ya amince da nada Samson Siasia a matsayin kocin matasa 'yan kasa da shekaru 23, wanda Fatai Amo zai taimaka masa wajen gudanar da aikin.