An saki dan wasan Sheffield daga kurkuku

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An kama Evans ne da laifin yin fyade

An sallami tsohon dan wasan Sheffield United, Ched Evans, daga kurkuku bayan ya yi rabin wa'adin da aka dibar masa na shekaru biyar.

A watan Aprilun shekarar 2012 ne aka kama Evans, dan shekaru 25 a duniya, da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 19 fyade a watan Mayun 2012.

Shugaban Sheffield United Nigel Clough ya gana da manyan jami'an kulob din don tattauna wa kan yiwuwar komawar Evans kungiyar.

Sai dai kusan mutane 150,000 suka sanya hannu a kan wata takarda a shafin intanet domin yin adawa da komawar Evans kulob din.

Karin bayani