Newcastle ta shirya a kan Ebola

Image caption Alan Pardew ya ce sun shirya sosai domin tunkarar ebola

Manajan Newcastle United Alan Pardew ya ce kulob din yana shiri sosai don yin rigakafin cutar ebola ko da 'yan kasashen Africa da ke yi masa wasa sun dawo daga kasashensu na asali.

Cheick Tiote da Papiss Cisse na cikin 'yan wasan kungiyar da suka buga wasannin cancantar shiga gasar cin kofin kasashen nahiyar Africa.

Alan Pardew ya ce ba za su yi sakaci game da batun na ebola ba.

Ya ce: " 'yan wasa ne masu matukar muhimmanci a gare mu, don haka likitanmu ya yi nazari sosai kan abubuwan da ka-je-su-komo idan suka dawo".

Pardew ya kara da cewa kulob din ya dauki dukkan matakan kiwon lafiyar da suka kamata domin kula da 'yan wasan da iyalansu da zarar sun dawo.

Tiote yana cikin 'yan wasan da suka bugawa Ivory Coast a fafatawar da suka yi da DR Congo, yayin da shi kuma dan kasar Senegal, Cisse ya buga a wasan da kasar ta yi da Tunisia.

Karin bayani