'Ban san lokacin da Costa zai warke ba'

Diego Costa Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sai a tsakiyar watan Nuwamba a ke sa ran Costa zai dawo buga tamaula

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce ba shi da tabbacin lokacin da Diego Costa zai gama jinya ya dawo buga wa kulob din tamaula.

Costa, mai shekaru 26, ya zura kwallaye tara a wasanni bakwai da ya buga wa Chelsea, amma bai buga karawar da suka doke Crystal Palace 2-1, saboda raunin da ya ji.

Mourinho ya ce "Ina da tabbacin dan wasan zai buga wa Spaniya wasan neman tikitin shiga gasar cin Kofin Nahiyar Turai da za su buga a tsakiyar watan Nuwamba".

A fafatawar da suka yi da Crystal Palace a wasan Premier ranar Asabar, Loic Remy ne ya maye gurbin Costa, daga baya Didier Drogba ya shiga wasan.

Spaniya za ta kara da Belarus a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai ranar 15 ga watan Nuwamba, sannan ta buga da Jamus a wasan sada zumunta kwanaki biyu tsakani.