Sa a muka samu a kan QPR — Rodgers

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto
Image caption Rodgers ya ce da kwarewa suka samu maki uku a kan QPR

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce sa a suka samu a kan QPR a karawar da suka doke su 3-2 a gasar Premier wasan mako na takwas.

QPR ta samu damarmakin da ya kamata ta zura kwallaye a raga, kafin a zura kwallaye hudu yayin da ya rage saura minti takwas a tashi wasa daya bai wa Liverpool damar lashe karawar.

Rodgers ya ce "Ya kamata ace QPR ce ta lashe wasan da muka yi, mun samu nasara ne a wasan kawai, amma mun nuna kwarewa daga bangaren 'yan wasan mu".

Nasarar da Liverpool ta samu ta sa tana mataki na biyar da maki 13 a teburin Premier, yayin da QPR ke matsayi na 20 da maki hudu kacal.