Kiris ya rage Messi ya kafa tarihin cin kwallo

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura kwallaye biyu ya rage wa Messi ya kafa tarihin dan wasan da ya fi zura kwallo a La Liga

Lionel Messi yana daf da kafa tarihi a matsayin dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye a gasar La Liga Spaniya bayan da suka doke Eibar ranar Asabar.

Bayan da suka dawo daga hutun rabin lokaci ne babu ci, Messi ya bai wa Xabi kwallon da nan take ya zura a ragar Eibar.

Dan kwallon Brazil Neymar ne ya kara ta biyu, lokacin da ya samu tamaula daga hannun mai tsaron bayan Barcelona Dani Alves.

Wasa na kai wa minti na 74 ne Messi ya zari kwallo ya kuma ratsa cikin 'yan bayan Eibar ya kuma zura kwallo ta uku a karawar, kuma ta 250 da ya zura a gasar La Ligar.

Messi, mai shekaru 27, saura kwallo daya ya kamo dan wasan Athletic Bilbao Telmo Zarra, wanda ya kafa na wanda ya fi yawan zura kwallaye a raga daga shekarar 1940 zuwa 1950.

Barcelona za ta kara da Real Madrid a wasan El Clasico ranar Asabar, kuma idan Messi ya kara zura kwallaye biyu a raga, zai zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a La Liga.