Nasarawa United ta doke Kano Pillars 1-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Saura wasanni hudu a kammala gasar Premier Nigeria

Nasarawa United ta doke Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 34 da suka buga ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka fafata, Enyimba har gida ta doke Kaduna United da ci daya da nema, a inda Sharks ta zura wa Sunshine Stars kwallaye 4-1.

Heartland ta samu maki uku bayan da ta doke Warri Wolves da ci daya mai ban haushi, inda Nembe City ta kwaso kwallaye uku da nema a karawar da suka yi da Elkanemi a jihar Kano.

Karawa tsakanin Gombe United da Giwa tashi wasa suka yi kunnen doki, yayin da Enugu Rangers ta casa Crown FC har gida da ci 3-0.

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi da maki 56, inda Warri Wolves ke mataki na biyu da maki 55, sai Enyimba da maki 54 a matsayi na uku.

Ga sakamakon wasannin mako na 34 da suka buga:

Akwa United 2 vs 1 Dolphin Bayelsa United 3 vs 0 Taraba FC Crown FC 0 vs 3 Enugu Rangers El-Kanemi Warriors 3 vs 0 Nembe City FC Gombe United 1 vs 1 Giwa FC Heartland 1 vs 0 Warri Wolves Kaduna United 0 vs 1 Enyimba FC Lobi Stars 2 vs 1 Abia Warriors Nasarawa United 1 vs 0 Kano Pillars Sharks 4 vs 1 Sunshine Stars