An kama wanda ya saki na'ura a wasan City

Manchester City Drone Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan sanda sun ji tsoron kada jirgin ya haddasa 'yan kallo su firgita

An kama wani mutun da ya saki wani dan karamin jirgi mai shawagi a sararin sama a filin Ettihad lokacin da Manchester City ke karawa da Tottenham a gasar Premier.

'Yan sandan Greater Manchester sun kama mutumin mai shekaru 41, dan Nottingham a daf da wurin da ake ajiye motoci na Asda.

Mutane da dama sun tsinkayi na'urar ne a lokacin da take shawagi a saman filin Ettihad lokacin da City ta lashe karawar da ci 4-1.

Mahukuntan sun ce sun kama mutumin ne domin ya karya ka'idojin zirga zirgar sararin samaniya, amma an bada shi beli na tsawon makwonni takwas.

Jami'an 'yan sanda sun ce sun kama mutumin ne domin na'urar da ya saka za ta iya haddasa firgici da hada yamutsi a filin wasan da zai iya sa aji rauni ko asarar rayuka.