Ya yi wuri a fara yabona - van Gaal

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manchester Unitred za ta ziyarci West Brom a gasar Premier

Louis van Gaal ya ce bai kamata a fara kimanta nasarorin da ya ke samu a Manchester United ba, watanni uku da kama aiki.

Lokacin da kocin ya karbi ragamar horas da United a watan Yuli, ya ce zai bi salon da zai dawo da tagomashin kungiyar a idon duniya.

United ta samu nasara a wasannin Premier data buga, sannan aka doke ta wasanni biyu da hakan yasa take mataki na shida a teburin Premier.

Van Gaal na fatan doke West Brom a karawar da za su yi ranar Litinin, hakan zai sa ta lashe wasanni uku a jere a karon farko a 2014.

Sai dai kocin dan kasar Netherlands bai amince ba da cewar United na taka rawar data dace, duk da doke West Ham da Everton da suka yi.