Kaicon Victor Moses, in ji Garry Monk

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Monk ya ce Moses bai kyauta ba

Kocin Swansea Garry Monk ya ce Victor Moses ya yi faduwar gangan ne domin hakan ya sanya a ba Stoke bugun fenareti, yana mai cewa "kaiconsa da ya yi hakan".

Kulob din Stoke dai ya doke Swansea 2-1 a filin wasa na Britannia, kana an hukunta dan wasansa Angel Rangel bayan ya yi wa Moses mugunta.

Kocin kulob din, wanda bai lashe wasa a gasar zakarun Turai biyar ba, ya ce: "bai kamata Moses ya rika faduwa da gangan ba; bai kamata ya rika yin cuta ba."

Sai dai kocin Stoke Mark Hughes ya bayyana kalaman da Monk ya yi a matsayin wadanda "ba za a amince da su ba".

Karin bayani