UEFA ta wanke Arsenal daga laifi

Arsenal flare Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Uefa ta wanke Arsenal daga laifin data tuhumeta a karawa da Galatasaray

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai, UEFA, ta wanke Arsenal daga tuhumar da ta yi mata a kasa hana 'yan kallo jefa abin dake tsartsatsin wuta a karawar da ta yi da Galatasaray.

Sai dai hukumar ta ci tarar Galatasaray fam 39,570 saboda samun 'yan kallonta da laifin kawo tarnaki a lokacin karawar.

A hukuncin da hukumar ta sanar ta ce Galatasaray za ta biya duk wata barnar da a ka yi a filin wasa na Emirates.

Tun farko UEFA ta tuhumi Arsenal da kasa caje 'yan kallo a lokacin da za su shiga filin wasanta lamarin da ya sa aka shiga filin da abin da ke sa tartsatsin wuta.

Arsenal ce ta lashe wasan da suka kara ranar 1 ga watan Oktoba da ci 4-1, za kuma ta ziyarci Istanbul a karawa ta biyu ranar 9 ga watan Disamba.