Bale ba zai buga karawa da Liverpool ba

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale zai yi jinyar rauni tare da Sergio Ramos

Gareth Bale ba zai buga wa Real Madrid karawar da za suyi da Liverpool a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba ba, saboda raunin da ya ji.

Bale, mai shekaru 25, ya ji rauni a kafarsa, kuma ba a saka shi a wasan da Madrid ta doke Levante a gasar La Liga ranar Asabar ba.

Dan kwallon ba ya cikin 'yan wasa 20 da Madrid ta bayyana za su buga mata karawar, Shi ma Sergio Ramos ba zai samu buga wasan ba, saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.

Bale ya buga wa Wales wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da suka kara da Bosnia-Hercegovina ranar 10 ga watan Oktoba da kuma Cyprus kwanaki uku tsakani .

Real Madrid ta lashe wasanni biyu data buga a gasar cin kofin zakarun Turai na bana, a inda Liverpool ta samu nasara a wasa daya aka kuma doke ta wasa daya.