An lalata filin wasan Shakhtar Donetsk

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A baya dai an taba lalata filin wasan na Shakhtar Donetsk

Rikicin da ake yi a Ukraine ya yi sanadiyar lalata filin wasan Shakhtar Donetsk da ke Donbass .

Mutanen da ke aiki a filin sun ce wasu fashe-fashe da suka faru a kusa da shi sun yi sanadiyar rugujewar bangaren gabas da na yamma, kana suka rusa wani bangare na babbar kofar da aka yi ta da gilasai.

Manajan kungiyar, Vadyn Gunko, ya ce :"Muna yin gargadi ga mazauna yankin da su guji matsowa wurin da filin wasan yake domin kuwa ba mu da tabbacin tsaron lafiyarsu."

A watan Yuli ne kungiyar ta sauya filin wasanta saboda rikicin da ake yi as kasar.

Da ma dai an taba lalata filin wasan, wanda ke daukar mutane 52,000, lokacin da dakarun gwamnati da 'yan a-ware suka fafata a watan Agusta.

Karin bayani