CSKA Moscow da Man City sun buga 2-2

Manchester City Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Manchester City ta kasa kamo bakin zaren buga gasar zakarun Turai

Manchester City ta tashi wasa da CSKA Moscow 2-2 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka fafata a Moscow ranar Talata.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun Sergio Aguero a minti na 29, kafin daga baya Milner ya kara ta biyu saura mintuna takwas a tafi hutu.

CSKA Moscow ta fara farke kwallon farko ta hannun Seydou Doumbia, kafin daga baya ta farke ta biyu a dukan fenariti da Bedras Natcho ya buga.

Sakamakon wasan yasa Manchester City cikin tsaka mai wuya a neman kai wa wasan zagaye na biyu na cin kofin zakarun Turai.

Bayern Munich ce ke matsayi na daya a teburi, sai Roma da take biye da ita kafin Manchester City.