El Clasico ba daukar kofi ba ne - Enrique

Barcelona Team Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Barcelona

Luis Enrique ya ce karawar da Barcelona za su yi da Real Madrid ranar Asabar da ake yi wa lakabin El Clasico ba wasan daukar kofi ba ne.

Barcelona wadda take mataki na daya a teburin La Liga, za ta ziyarci Bernabeu domin fafatawa da Madrid, akwai dai tazarar maki hudu tsakaninsu.

Har yanzu kwallo bata shiga ragar Barcelona ba, yayin da Madrid ta zura kwallaye 25 a wasanni biyar baya data buga.

Enrique ya ce "Wannan karawar da za muyi ba shi ne zai nuna wanda zai lashe kofin La Liga bana ba, domin akwai wasanni da dama da za mu buga a gaba".

Real Madrid za ta kara da Liverpool a Ingila ranar Laraba, yayin da Barcelona ta doke Ajax da ci 3-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Talata.