Real Madrid ta doke Liverpool 3-0 har gida

Liverpool Real Madrid Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona ranar Asabar

Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci 3-0 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka buga a filin Anfield ranar Laraba.

Madrid ta fara zura kwallonta na farko ne ta hannun Ronaldo a minti na 23, kafin daga baya Benzema ya kara ta biyu a minti na 30 da kuma ta uku a minti na 41.

Wannan nasarar yasa Madrid tana matsayi na daya a teburin rukuni na daya da maki tara, a inda Liverpool ke mataki na uku da maki uku, bayan buga wasanni uku.

Ranar Asabar ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a karawar da ake kira El Clasico a gasar cin kofin La Liga.

Ga sakamakon sauran wasannin gasar cin kofin zakarun Turai:

Atl Madrid 5 - 0 Malmö FF Olympiakos 1 - 0 Juventus Liverpool 0 - 3 Real Madrid Ludo Razgd 1 - 0 FC Basel Bayer Levkn 2 - 0 Zenit St P Monaco 0 - 0 Benfica L Galatasaray 0 - 4 Bor Dortmd Anderlecht 1 - 2 Arsenal