Kompany ya soki Uefa saboda 'yan kallo

Image caption Komapany ya ce ba a kyauta musu ba

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya soki Hukumar kwallon kafar Turai saboda hana masu goya musu baya shiga filin wasa a karawar da suka tashi 2-2 da CSKA Moscow.

Kompany ya ce an hukunta kungiyarsu ba tare da dalili ba, bayan da suka gwabza a filin wasan CSKA Moscow wanda babu masu kallo da yawa a cikinsa.

Uefa ce dai ta hana masu kallo da yawa shiga filin saboda a baya an samu tarzoma a cikinsa.

Company ya ce: "me ya sa aka hana 'yan kallo shigowa cikin filin. Wanne laifi masu goyon bayanmu suka yi da za a hana su? Gaskiya ba a yi mana adalci ba".

Magoya bayan CSKA dai sun kalli wasan daga babban mazauni da ke filin wasan duk da cewa an hana masu kallo shiga filin.

Karin bayani