An sallamo Diego Costa daga asibiti

Diego Costa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho ya ce bai san lokacin da Costa zai dawo buga tamaula ba

Likitoci sun sallami dan kwallon Chelsea, Diego Costa, daga asibiti bayan da ya sha fama da rashin lafiya.

Dan kasar Spaniyan ya yi fama da ciwon ciki ne bayan ya koma Ingila daga wasan da ya buga wa kasarsa.

Kazalika yana yin jinyar raunin da ya ji lokacin da yake wa Spaniya wasa, bai kuma buga wa Chelsea karawar da ta doke NK Maribor 6-0 ranar Talata ba.

Costa, mai shekaru 26, ana tunanin ba zai murmure ba kafin karawar da Chelsea za ta yi da Manchester United a Gasar Premier a Old Trafford ranar Lahadi.

Chelsea tana matsayi na daya a tebutin Premier, yayin da Manchester United ke mataki na shida bayan buga wasanni takwas.