El Clasico: Ba na hamayya da Messi - Ronaldo

El Clasico
Image caption Real Madrid ce za ta karbi bakuncin Barcelona ranar Asabar

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce ya fi maida hankali kan yadda za su doke Barcelona, ba kokarin taka rawa fiye da Messi ba a karawar da za suyi ranar Asabar.

Ronaldo ya zura kwallaye 15 daga cikin wasanni bakwai da ya buga a gasar La Ligar bana, a inda Messi ke kokarin karya tarihin yawan zura kwallo a gasar.

Sai dai kuma Ronaldo ya yi watsi da zargin da ake cewa akwai adawa mai zafi tsakaninsa da Messi.

Ronaldo, mai shekaru 29, ya ce "Zan buga wasa ne tsakaninmu da Barcelona ba Messi ba a ranar Asabar".

Karawar da za suyi da ake wa lakabin El Clasico, Xabi ya buga fafatawa karo 40, sai Casillas da ya buga sau 35, yayin da Iniesta ya buga karo 29, Messi ya buga kwafsawa sai 28.

Real Madrid ce ke da rinjaye a haduwar bangarorin biyu, inda ta zura wa Barcelona kwallaye 385 a fafatawar El Clasico, da tazarar kwallaye 14 tsakaninsu.