'Ina nan kan batuna, da gangan Moses ya fadi'

Stoke Swansea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar kwallon kafa ta bukaci kocin ya yi karin jawabi

Kocin Swansea ya ce har yanzu yana nan kan batun da ya yi cewa da gangan Victor Moses ya fadi har aka bayar da fenaritin da Stoke ta doke su 2-1 a gasar Premier.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta rubuta wa Monk wasika, inda ta bukaci ya yi mata kan kalaman da ya yi bayan an tashi wasan cewa, Moses ya yi kwange.

Har yanzu hukumar ba ta yanke matsaya ba, ko za ta dauki mataki bisa batun da ya yi.

Monk ya ce "Ina matukar kaunar kungiyata, kuma duk lokacin da aka yi min rashin adalci, lallai kam yana daga cikin aiki na in ce ba'a kyauta mana ba".

Hukumar kwallon kafar ta bai wa kocin daga nan zuwa 27 ga watan Oktoba ya amsa wasikar da ta rubuta masa.