Zan so a kalubalanci kujerar Blatter - Dyke

Greg Dyke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dyke ya ce ya kamata a samu sauyin shugabancin FIFA

Shugaban hukumar kwallon kafar Birtaniya Greg Dyke ya ce zai so ya ga an samu wanda zai kalubalanci Sepp Blatter, a lokacin zaben shugaban FIFA a shekara mai zuwa.

Blatter duk da tabbacin da ya bayar a baya cewa zai sauka daga jagorantar FIFA a 2013, ya fada a watan Satumba cewar zai sake neman cigaba da shugabantar hukumar.

Dyke ya fada a wata kafar yada labarai "Blatter shugaba ne, amma muna bukatar canji, hakan kuma ba zai yi wu ba sai an samu wanda zai kada shi a takarar shugaban FIFA".

Blatter, mai shekaru 78, ya tattauna tare da Dyke akan batutuwa da dama, ciki har da batun kar bar bakuncin kofin duniya da Qatar za ta yi a 2022.

Shugaban kwallon kafar Ingila ya bayyana fatansa cewar yana son ganin wani ya fito neman kujerar shugabancin FIFA domin karawa da Blatter a watan Mayun shekara mai zuwa