Magoya bayan Liverpool sun yi zanga-zanga

Liverpool Supporters Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool ta tashi wasa babu ci da Hull a Premier ranar Asabar

Magoya bayan kulob din Liverpool sun yi zanga-zanga a filin wasa na Anfield akan tsadar tikitin kallon wasa, lokacin da su ka tashi wasa babu ci da Hull ranar Asabar.

A wani bincike da BBC ta gudanar kan tsadar tikitin kallon kwallo, tikiti mafi arahar kallon wasan Liverpool a gida ya kai fam 37, inda matsakaicin tikitin kallon Premier shi ne sama da fam 28.

'Yan kallo a filin Anfield sun daga kyallaye dauke da sakon dake cewa magoya baya ba masu cinikayya ba ne.

Arsenal ce kan gaba wajen tsadar tikiti da ya kai fam 1,014, sai Tottenham fam 765, Chelsea fam 750, sai kuma Liverpool ta hudu a tsadar tikitin kallon tamaula.

An tuntubi kulob din Liverpool kan zanga-zangar da magoya bayanta suka yi, amma har yanzu ba suce komai ba.