Labaran da suka fi jan hankali a Premier

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Labaran da suka fi jan hankali a gasar Premier wasan mako na 9

Manchester United ta raba maki da Chelsea

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya yaba da kwazon 'yan wasansa, bayan da suka tashi wasa 1-1 da Chelsea. Drogba ne ya fara zura kwallo kafin Robin van Persie ya farke daf da a tashi wasa, kuma hakan yasa United ta tsawaita wasanni hudu a gida ba a doke ta ba. United ta yi murnar farke kwallonta a Old Trafford tamkar ita ce ta lashe wasa, kuma hakan na nunin cewar kulob din na daf da dawo da tagomashinsa.

'Yan wasan Afirka na nuna kwarewarsu a Premier

Kwallon da Drogba ya ci United, ita ce ta farko da ya zura a Premier tun Maris 2012, bayan da ya samu buga karawar sakamakon raunin da Diego Costa ya ji. Shi ma dan wasan Kamaru Samuel Eto yana daga cikin 'yan wasa daga Afirka da ya zura kwallo a raga a gasar Premier wasan mako na tara. Eto ya zura kwallaye biyu a karawar da Everton ta doke Burnley da ci 3-1, kiris ya rage ya kara ta uku, bayan da kwallon da ya buga ta doki turke.

Pochetino na fuskantar kalubale a Tottenham

Tsohon dan wasan Argentina Mauricio Pochettino ya jagoranci Southampton taka rawar gani a gasar Premier a shekarar farko da ya fara koci a Ingila, wanda hakan ne yasa Tottenham ta dauko shi aiki. Sai dai ya fara fuskantar kalubale bayan da Newscastle ta doke su 2-1 a gida, inda koci Alan Pardew ya samu sa'ida daga matsin da yake sha daga magoya bayan Newcastle. Tottenham tana matsayi na 11 a teburin Premier, a inda Pochetino yake tambayar tunanin 'yan wasansa ko suna sane da yanayin da za su fada kuwa? Ganin wannan ne karo na uku da aka doke su a gida a gasar bana.

Magoya bayan West Ham sun kwana cikin farin ciki

West Ham tana cikin jerin kungiyoyi hudun farko dake teburin Premier, bayan da suka doke Manchester City da ci 2-1 ranar Asabar.Tun a baya magoya bayan West Ham sun bukaci a kori koci Sam Allardyce bisa kai wa da kyar a gasar bara da kuma kasa taka kwallo mai kayatarwa daga 'yan wasa. Amma sai gashi a kakar bana kulob din ya sauya salon wasansa da yawan zura kwallo, inda ya lashe wasanni biyar kuma karon farko tun bayan shekaru 15 da kulob din ya taka irin wannan rawar, kuma hakan yasa West Ham tana cikin 'yan hudun farko a teburin Premier bana.

Arsenal ta ci moriyar kuskuren 'yan wasan Sunderland

Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez ne ya ci moriyar kuskuren da masu tsaron bayan Sunderland suka yi da ya bashi damar zura kwallaye biyu, kuma hakan yasa ya zura kwallaye biyar a wasanni bakwai da ya buga a Premier bana. Kocin Sunderland Gus Poyet ya so ace 'yan wasansa sun faranta ran magoya baya sun doke Arsenal, domin satin da ya gabata kwallaye 8-0 Southampton ta doke su, amma sai gashi kwararen mai tsaron baya Wes Brown ya yi kuren da Sanchez ya zura musu kwallon farko, kafin gola Vito Mannone ya yi kure na biyu kuma Sanchez ya kara ci, aka tashi wasa Arsenal nada ci 2-0.