An jefi kocin CSKA Sofia da kankara

CSKA Sofia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan CSKA Soyiya sun ce kocin lambo ya yi

Magoya bayan kulon din Levski Sofia sun ce kocin CSKA Sofia Stoycho Mladenov lambon faduwa ya yi lokacin da aka jefe shi da kankara daga sashin magoya bayan kulob din.

Mladenov ya fadi wanwar a karawar da suka lashe wasa da ci 3-0, daga baya ya sanar da cewa suma ya yi da aka jefe shi.

Shugaban magoya bayan Levski, Vladimir Vladimirov ya ce "Yara ma na wasan jifa da kankara, bai taba jin an jefi wani har ya suma ba".

Koci Mladenov ya ce yana da takaddar da likita ya auna shi da girman raunin da ya ji, zai iya bai wa hukumar kwallon Bulgeria idan ta bukuta.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar Bulgeria zai tattauna kan dalilan da yasa aka jefi kocin da kankara ranar Talata.