Courtois ne ya ceci Chelsea - Shaw

Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shaw ya ce United za ta dawo da tagomashinta a bana

Luke Shaw ya ce golan Chelsea Thibaut Courtois ne ya ceci su a karawar da suka tashi kunnen doki da Manchester United ranar Lahadi.

Chelsea ce ta fara zura kwallo ta hannun Didier Drogba, bayan an dawo daga hutun kafin United ta farke kwallo ta hannu Robin van Persie daf da a tashi wasa.

Courtois ya tare kwallayen da van Persie ya kusa zura wa a raga kafin a tafi hutu da bayan an dawo da kuma kwallon da Angel di Maria ya sheka masa.

Golan Belgium wanda ya kwashe shekaru uku aro a kulob din Atletico Madrid, ya maye gurbin Peter Cech a matsayin golan da ya ke tsare wa Chelsea raga.

Shaw ya ce "Mun samu damar makin zura kwallaye a raga, wanda golan Chelsea ya dunga hana su shiga, musamman hare-haren Robin da na Adnan Januzaj".