Van Gaal ya yabawa 'yan Man U

Hakkin mallakar hoto
Image caption Louis van Gaal ya ce 'yan wasansa sun jajirce

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya jinjinawa 'yan kwallonsa saboda jajircewar da suka yi a wasan suka yi da Chelsea ranar Lahadi.

A mintuna na 87 ne dai Van Persie ya farkewa kungiyar kwallon da dan wasan Daley Blind, lamarin da ya sa suka tashi 1-1.

Van Gaal ya ce,"Abin alfahari ne yadda suka taka leda duk da kalubalen da suka fuskanta."

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce wasan bai yi musu dadi ba, yana mai cewa sun yi wasu kura kurai ne.

Karin bayani