Tawagar Argentina ta gayyato Carlo Tevez

Carlo Tevez Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Tevez na taka rawa a kungiyar Juventus ta Italiya

Argentina ta gayyato Carlo Tevez cikin tawagar 'yan kwallon kafarta a karawar wasan sada zumunci da za su buga da Croatia da kuma Portugal a watan gobe.

Rabon da Tavez, mai shekaru 30, tsohon dan wasan Manchester United mai taka leda a Juventus ya buga wa Argentina wasa tun a shekarar 2011.

Kuma karawar da suka yi da Uruguay a gasar cin Copa America wasan daf dana kusa da karshe ne wasansa na karshe da Argentina.

Argentina za ta kara da Croatia ranar 11 ga watan Nuwamba a Landan, sannan ta fafata da Portugal a Manchester mako guda tsakani.

Ga sunayen 'yan wasan Argentina da za su buga mata wasan:

Masu tsaron raga: Sergio Romero (Sampdoria), Willy Caballero (Manchester City), Nahuel Guzman (Tigres)

Masu tsaron baya: Nicolas Otamendi (Valencia), Cristian Ansaldi (Atletico Madrid), Facundo Roncaglia (Fiorentina), Marcos Rojo (Manchester United), Martin Demichelis (Manchester City), Pablo Zabaleta (Manchester City), Federico Fazio (Tottenham), Federico Fernandez (Swansea), Ezequiel Garay (Zenit)

Masu buga tsakiya: Javier Mascherano (Barcelona), Roberto Pereyra (Juventus), Lucas Biglia (Lazio), Angel Di Maria (Manchester United), Erik Lamela (Tottenham), Javier Pastore (PSG), Enzo Perez (Benfica), Nicolas Gaitan (Benfica)

Masu zura kwallo a raga: Lionel Messi (Barcelona), Carlos Tevez (Juventus), Gonzalo Higuain (Napoli), Sergio Aguero (Manchester City)