Benteke bai gama murmurewa ba - Lambert

Christian Benteke Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Benteke bai buga gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil ba

Kocin Aston Villa Paul Lambert ya ce Christian Benteke yana bukatar buga wasanni shida zuwa bakwai kafin ya murmure ya koma kan ganiyarsa.

Dan wasn mai shekaru 23, ya yi jinyar raunin da ya ji a cikin watan Afirilu a karawar da Queens Park Rangers ta doke su 2-0.

Lambert ya ce "Raunin ya janyo wa dan wasan koma baya, saboda haka yana bukatar buga wasanni da dama kafin ya dawo kan ganiyarsa.

Benteke ya zura kwallaye 34 a raga a wasanni 69 da ya buga wa Villa, kuma har yanzu bai dawo kan ganiyarsa ba, bayan jinyar raunin da ya hana shi buga gasar cin kofin duniya.

Rashin buga wa Villa tamaula da Benteke ba ya yi yasa bata zura kwallaye a gasar Premier ba, kuma an doke ta wasanni biyar a jere.