An fitar da sunayen 'yan takarar Ballon d'Or

Ballon d'Or Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar 12 ga watan Janairun badi ne za a bayyana gwarzon kwallon kafar bana

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar da sunayen 'yan wasa 23 da za a zabo gwarzon dan kwallon duniya na shekarar nan a cikinsu, wato kyautar Ballon d'Or.

Kwamitin kwallon kafa na FIFA da rukunan masana harkar taka leda daga mujallar Faransa ne suka zakulo sunayen 'yan wasan da suka yi fice wajen buga tamaula a bana.

Masu horar da 'yan wasa da Kyaftin din mambobin hukumar FIFA da kuma fitattun 'yan jarida ne ke zaben dan wasan da ya fi fice a duniya

A ranar 1 ga watan Disamba ne FIFA za ta sanar da sunayen 'yan wasa uku da za a fitar da gwarzon shekarar nan a cikinsu a Zurich ranar 12 ga watan Janairun 2015.

FIFA ta kuma fitar da sunayen masu horar da 'yan wasa da za a zabo wanda yafi fice a shekarar 2014.

Ga sunayen da 'yan wasa 23 da za a zabo gwarzon dan kwallon bana a cikinsu:

Gareth Bale (Wales), Karim Benzema (France), Diego Costa (Spain), Thibaut Courtois (Belgium), Cristiano Ronaldo (Portugal), Angel Di Maria (Argentina), Mario Goetze (Germany), Eden Hazard (Belgium), Zlatan Ibrahimovic (Sweden), Andres Iniesta (Spain), Toni Kroos (Germany), Philipp Lahm (Germany), Javier Mascherano (Argentina), Lionel Messi (Argentina), Thomas Mueller (Germany), Manuel Neuer (Germany), Neymar (Brazil), Paul Pogba (France), Sergio Ramos (Spain), Arjen Robben (Netherlands), James Rodriguez (Colombia), Bastian Schweinsteiger (Germany), Yaya Toure (Côte d'Ivoire).

Ga sunanyen masu horar da 'yan wasa da za a zabo wanda yafi fice a bana:

Carlo Ancelotti (Italy/Real Madrid CF), Antonio Conte (Italy/Juventus FC/Italy national team), Pep Guardiola (Spain/FC Bayern Munich), Juergen Klinsmann (Germany/ USA national team), Joachim Loew (Germany/Germany national team), Jose Mourinho (Portugal/Chelsea FC), Manuel Pellegrini (Chile/Manchester City FC), Alejandro Sabella (Argentina/Argentina national team), Diego Simeone (Argentina/Atletico Madrid), Louis van Gaal (Netherlands/Netherlands/Manchester United FC).