FIFA ta bai wa Nigeria wa'adin nan da Juma'a

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo biyu FIFA tana dakatar da Nigeria a bana

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bai wa Nigeria daga nan zuwa Juma'a cewar ta janye hukuncin da wata babbar kotu a Jos ta yanke na rushe zaben NFF ko kuma ta hukunta ta.

A wata wasika da FIFA ta rubuta wa Nigeria ranar Talata ta bukaci kasar da ta bi umarnin da ta ba ta kafin 31 ga watan Oktoba.

FIFA ta bukaci a mayar da Shugabancin hukumar NFF wanda zaben 30 ga watan Satumba ya dora Amaju Pinnick a matsayin shugaban kwallon kafar kasar.

Hukuncin da FIFA za ta dauka kan Nigeria zai hada da dakatar da ita shiga duk wata harkar kwallon kafa a duniya.

Hakan kuma zai iya hana Nigeria shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, idan ta samu gurbin buga gasar wadda take rike da kofin.

A shekarar nan sau biyu FIFA tana dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa, ta kuma gargade ta da kada a sake samun rikici a hukumar.