Gattuso zai ci gaba da horarwa a Crete

Gennaro Gattuso Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gattuso ya ce zai yi kokarin ganin kulob din ya taka rawar gani

Tsohon dan kwallon Italiya Gennaro Gattuso ya sauya ra'ayin yin ritaya daga horar da kungiyar kwallon kafa ta Crete.

Gattuso, mai shekaru 36, ya sanar da cewar zai bar horar da Crete, bayan da kulob din Asteras Tripolis ya doke su har gida da ci 3-2 ranar Lahadi.

Doke kulob din Crete da aka yi a karshen mako, ya sa ta koma mataki na bakwai a gasar Girka da maki tara tun lokacin da Gattuso ya koma kulob din.

Kocin ya ce "Na hakura zan ci gaba da jagorantar Crete da fatan zan samu goyon baya daga 'yan wasa da magoya baya".

A watan Mayun 2013 ne kulob din Sion dake Swistzerland ya sallami Gatuso, bayan wasanni 11, Palermo ma ta sallame shi a Satumba bayan wasanni shida kacal.