'Yan wasan Newcastle na goyon bayan Pardew

Alan Pardew
Image caption Newcastle ta fara gasar Premier bana da kafar hagu

Mai tsaron bayan kulob din Newcastle Daryl Janmaat ya ce suna goyon bayan Alan Pardew, kuma ba sa bukatar a kawo musu sabon mai horar da tamaula.

Magoya bayan kulob din sun yi ta kiraye-kirayen a sallami Pardew, bayan da Newcastle ta kasa lashe wasanni biyar a gasar Premier bana.

Janmaat ya ce an rage matsawa kocin ne, bayan da suka doke Leister da Tottenham, da hakan ya kara musu kwarin giwa.

Mai tsaron bayan, dan kasar Netherlands da ya koma Newcastle a bana, ya kara da cewa kocin ya fuskanci adawa mai zafi, amma yanzu muna murnar samun maki a wasannin mu.

Newcastle za ta ziyarci Ettihad domin karawa da Manchester City a gasar League Cup wasan zagaye na hudu ranar Laraba.