Ancelotti ya ce raunin Bale bai yi muni ba

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale yana cikin 'yan wasan da ake zabo domin lashe kyautar gwarzon dan wasan bana na duniya

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya karyata rade radin da ake cewar raunin Gareth Bale mai muni ne da zai dade yana jinya.

Bale, mai shekaru 25, bai buga wa Real Madrid wasanni uku data buga ba, ciki har wasan El Clasico da ta doke Barcelona 3-1.

Dan wasan yana fama da jinyar rauni da ya ji a kafarsa, kuma ba zai buga gasar Copa del Rey da Madrid za ta buga da Cornella ranar Laraba ba.

Madrid za ta kara da Liverpool a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar 4 ga watan Nuwamba, ta kuma fafata da Granada da Rayo Vallecano kafin a tafi hutun wasanni.

Wales za ta kara da Belgium a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ranar 16 ga watan Nuwamba a Brussels.

Bale yana daga cikin 'yan wasa 23 da FIFA ta fitar domin zabo gwarzon dan wasa da yafi fice a duniya a bana.