Chelsea ta doke QPR da ci 2-1 a Stamford Bridge

Kulob din Chelsea ya ci gaba da zama a matsayi na daya a teburin Premier, bayan da ya doke QPR da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka buga ranar Asabar.

Chelsea ce ta fara zura kwallo ta hannun Oscar daga yadi 12 a minti na 32 da fara tamaula, bayan an dawo QPR ta farke kwallo ta hannun Charlie Austin.

Chelsea ta kara kwallo ta biyu a dukan fenariti da Hazard ya buga, bayan da mai tsaron bayan QPR Eduardo Vargas ya yi masa keta a da'ira ta 18.

Har yanzu Chelsea ta ci gaba da rike matsayi na daya a teburin Premier da maki 26, bayan buga wasanni 10 a bana.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka buga:

Arsenal 3 - 0 Burnley Chelsea 2 - 1 QPR Everton 0 - 0 Swansea Hull 0 - 1 Southampton Leicester 0 - 1 West Brom Stoke 2 - 2 West Ham