Newcastle ta doke Liverpool da ci 1-0

Kungiyar Newcastle ta lashe Liverpool a gasar Premier wasan mako na 10 da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi ranar Asabar.

Newcastle ta zura kwallonta tilo ne ta hannun Ayoze Perez, bayan da mai tsaron bayan Liverpool Alberto Moreno ya yi kuskuren bar masa kwallo a gabansa.

Nasarar da Newcastle ta samu, ya sa ta lashe wasannin Premier biyu a jere, kuma gasar wasanni hudu da ta kara daban daban.

Liverpool ba ta samu damar makin zura kwallo a raga ba, in banda wadda Martin Skrtel ya sawa kwallo kai ta kuma yi waje.