Gareth Bale ya komo atisaye da Real Madrid

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ya koma atisaye da kulob din ranar Lahadi, domin tunkarar karawar da za su karbi bakuncin Liverpool ranar Talata a gasar cin kofin zakarun Turai.

Bale, dan wasan Wales, bai buga wa Madrid wasanni biyar ba, sakamakon jinyar raunin da ya yi.

Dan wasan da Madrid ta sayo mafi tsada a duniya daga Tottenham, bai buga wasan da Real ta doke Liverpool a Anfield ba, amma yana sa ran buga karawa ta biyu.

Real Madrid wadda ta dare matsayi na daya a teburin La Liga ta lashe wasanni 11 a dukkan karawar da ta fafata.

Kuma Madrid ce kan gaba a rukunin da ta ke a gasar zakarun Turai, bayan da ta lashe wasanni uku da ta buga.