Wilshare ba zai buga wasan Anderlecht ba

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wilshere zai iya murmurewa domin buga wa Arsenal wasanta na gaba

Jack Wilshare ba zai buga karawar da Arsenal za ta yi da Anderlecht ba a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata, sakamakon rashin lafiya.

Theo Walcott ya buga gasar Premier da Burnley ranar Asabar, yayin da Mesut Ozil da Mathieu Debuchy da kuma Olivier Giroud ke daf da dawo wa taka leda bayan jinyar rauni da suka yi.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce "Yan wasanmu da ke jinya sun kusa dawo wa buga mana wasa, hakan zai taimaka mana matuka".

Idan Arsenal ta doke Anderlecht zai ba ta tikitin kai wa wasan zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun Turai.