Ku ci gaba da goyon bayan Barca - Suarez

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karo na biyu Suarez yana buga wa Barca kwallo ana kuma doke su

Luis Suarez ya roki magoya bayan Barcelona da su ci gaba da mara wa kulob baya duk da doke su wasa biyu a La Liga da aka yi a jere.

Barcelona ta sha kashi a hannun Real Madrid a wasan El Clasico da ci 3-1, sannan Celta Vigo ta doke ta da ci daya mai ban haushi a gida ranar Asabar.

Haka kuma kulob din ya sauka daga matsayi na daya ya koma mataki na hudu a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninsu da Madrid wadda take ta daya a teburi.

Suarez, mai shekaru 27, ya ce "A ci gaba da mara mana baya, mun fi kowa son muga muna kokari a wasa domin aikinmu kenan".

Dan kwallon Uruguay ya koma Barcelona ne daga Liverpool, kuma ya kammala hukuncin dakatar da shi wasa tsawon watanni hudu da aka same shi da laifin cizo a gasar kofin duniya.