Nation Cup 2015: An bai wa Morocco wa'adi

Afcon 2015 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola ta kawo koma baya a harkar kwallon kafar Afirka

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta jaddada wa Morocco cewar ba za ta dage gasar cin kofin Afirka daga watan Janairu kamar yadda ta tsara ba.

Ta kuma ba ta wa'adin daga nan zuwa ranar Juma'a ta tabbatar idan ta na da sha'awar karbar bakuncin wasannin.

Tun farko Morocco ta bukaci CAF da ta dage gasar kamar yadda ta tsara, saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Wa'adin da CAF ta bai wa Morocco na daga nan zuwa 8 ga watan Nuwamba idan za ta karbi bukunci gasar, kuma shi ne wa'adin ga duk kasar dake da sha'awar maye gurbin Morocco.

CAF ta ce za ta fitar da matsaya kan kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka na badi ranar 11 ga watan Nuwamba.