Van Gaal ya soki Smalling da sakaci

Chris Smalling Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal ya ce ya kamata dan wasan yasan cewa wasan hamayya sai da kwantar da hankali

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya soki Chris Smalling da yin sakacin da ya sa aka ba shi jan kati a wasan hamayya da Manchester City.

An kori Smalling ne bayan da ya aikata laifuka biyu a fili, na farko kin matsawa daga jikin golan City Joe Hart lokacin da zai buga kwallo da kuma ketar da ya yi wa James Milner.

Manchester City ce ta lashe karawar da ci daya mai ban haushi, wanda Sergio Aguero ne ya zura kwallon a minti na 63.

Van Gaal ya ce "Idan kana buga wasan hamayya dole ka lura da salon wasanka, saboda haka Smalling ya yi shirme".

Duk da jan katin da aka bai wa United, ta kara kaimi inda ta kai hare-haren zura kwallo a raga, wanda golan City Joe Hart ya hana su shiga.