Walcott yana shirin tattauna wa da Arsenal

Theo Walcott Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Dan wasan ya dawo buga tamaula, bayan jinyar rauni da ya yi

Theo Walcott na shirye-shiryen tattauna wa da kulob din Arsenal akan batun tsawaita kwantiraginsa domin ya ci gaba da buga wa kulob din tamaula.

Walcott, mai shekaru 25, kwantiraginsa da kulob din zai kare ne a 2016, ya kuma dawo buga kwallo ranar Asabar, bayan jinyar watanni 10 da ya yi.

Arsene Wenger ya ce "Muna shirye-shiryen tattauna wa da shi domin tsawaita kwantiraginsa, koda yake yana da sauran yarjejeniyar shekara daya da rabi".

Dan kwallon Ingila ya koma Arsenal daga Southampton a shekarar 2006, inda ya zura kwallaye 45 daga wasanni 195 da ya buga.