Toure ya soki cin zarafin da aka yi masa

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya ce bai kamata a dawo da hannun agogo baya ba

Dan kwallon Manchester City Yaya Toure ya ce cin zarafin da aka yi masa ta kafar sada zumuntarsa abin takaici ne.

Tuni 'yan sanda suka fara binciken musgunawar da Toure ya ce an yi masa ta Twitter, sa'o'i kadan da ya farfado da shafinsa, bayan da ya jingine shi makwanni biyar baya.

Toure, mai shekaru 31, ya shaida wa BBC cewa "A gaskiya abin takaici ne, ya kamata muyi wani yunkurin dakatar da duk wani mai irin wannan dabi'ar".

"Ina son na wayar da kan masu irin wadannan halayen su gane cewar abin da suke yi bai kamata ba".