Sakho ya murmure daga jinyar da ya yi

Diafra Sakho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption dan wasan ya ji rauni ne a karawar da suka yi da Man City

Dan kwallon West Ham Diafra Sakho ya murmure daga jinyar da ya yi, zai kuma buga gasar Premier da za su kara da Aston Villa ranar Asabar.

Sakho, wanda ya koma kulob din daga Metz a bana, bai buga karawar da suka tashi 2-2 da Stoke City ranar Asabar ba.

Dan wasan ya ji rauni ne a kafata a wasan da suka buga da Manchester City da suka lashe da ci 2-1.

Haka kuma likitan West Ham Stijn Vandenbroucke ya ce dan kwallon da kulob din ya sayo mafi tsada a tarihi Andy Caroll shi ma yana daf da dawo wa daga jinya.

West Ham ta fara gasar Premier bana da kafar dama, inda ta dare matsayi na biyar da maki 17 bayan buga wasanni 10.