An ci tarar kocin Crystal Palace Warnock

Neil Warnock Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption FA ta kuma gargadi kocin da ya iya bakinsa

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar kocin Crystal Palace Neil Warnock fam 9,000, saboda jawabin da ya yi bayan kammala wasan da suka buga da Chelsea a Premier.

Warnock, mai shekaru 65, an zarge shi da cewar alkalin wasa Craig Pawson ya fifita 'yan wasan Chelsea a karawar da aka doke su 2-1 ranar 18 ga watan Oktoba.

Kocin wanda ya maye gurbin Tony Pulis, an kuma gargade shi da ya kauce wa yin irin wannan lafazin a gaba.

A wani jawabi da hukumar ta fitar ta ce, sakamakon binciken da kwamiti mai zaman kansa ya gudanar kan Neil Warnock, an ci tarar sa fam 9,000, saboda an same shi da laifin kalamun da basu kamata ba, bayan kammala wasa.