Galatasaray ta roki magoya bayanta

Galatasaray_flares Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption UEFA na jiran rahoton da alkalan wasa za su mika mata

'Yan wasan Galatasaray sun roki magoya bayansu su dena jefa tartsatsin wuta a filin wasa, bayan da sau biyu ana dakatar da wasan da suka kara da Borussia Dortmund a gasar kofin zakarun Turai.

Kyaftin din kulob din Selcuk Inan da Felipe Melo sai da suka je wajen magoya bayansu a daf da wajen da ake buga kwana suna basu hakuri a wasan da suka buga a Jamus ranar Talata.

Magoya bayan Dortmund sai kare kansu suka dinga yi, a lokacin da aka dinga jefa musu abubuwa masu tartsatsi a wurin da suke kallo.

An ci tarar Galatasaray fam 40,000 a karawar da Arsenal ta doke ta 4-1, bayan da hukumar kwallon kafar Turai ta sameta da laifin jefa abubuwa masu tartsatsin wuta fili.