World Cup 2022: 'Yan wasa ka iya kauracewa

Qatar 2022
Image caption Har yanzu ana takaddamar ranar da ya kamata a fara gasar kofin duniya

Shugabannin kungiyar masu buga tamaula ta duniya sun ce 'yan kwallon kafa za su iya kauracewa gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022, idan har ba a sauya lokacin buga gasar daga bazara ba.

Yanayi a Qatar yana kaiwa 40 a ma'aunin Celsius tsakanin Mayu da Satumba, koda yake har yanzu FIFA ba ta tsayar da ranar da za a fara gasar ba.

Sakatare janar na kungiyar 'yan wasan kwallon kafa FIFPro Theo van Seggelen, ya ce "ba za mu taba bari a saka rayuwar 'yan kungiyarmu a cikin garari ba, saboda haka za mu kalubalanci FIFA a kotu".

A shekarar 2010 ne aka baiwa Qatar izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2022. Amma sama da shekara guda ana takaddamar lokacin da ya kamata a buga gasar a kasar.

Manyan kulob -kulob din Turai sun bukaci FIFA da ta fara gudanar da gasar cin kofin duniya a watan Mayu, idan ba haka ba zai shafi gasar wasannin su.