Ronaldo ya nemi Madrid ta tsawaita kwantiraginsa

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo yana cikin yan kwallo 23 da ake sa ran zabo gwarzon dan wasa bana na duniya

Cristiano Ronaldo ya ce yana son a tsawaita kwantiraginsa a Real Madrid, duk da sauran shekaru hudu yarjejeniyarsu ta kare.

Dan kwallon Portugal, mai shekaru 29, an yi ta rade-radin zai koma wasa da Manchester United, kulob din da ya bari ya koma Madrid kan kudi fam 80 a shekarar 2009.

Ranar Laraba aka bai wa Ronaldo takalmin jinare, saboda zura kwallaye 31 da ya yi a gasar La Liga a bara.

Ronaldo sun raba kyautar dan kwallon da yafi zura kwallo a raga a nahiyar Turai tare da Luis Suarez wanda ya zura kwallaye 31 a gasar Premier a bara.