Roy Hodgson ya gayyci Saido Berahino

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hodgson ya ce daman dan wasan yana ranmu

A karon farko kocin Ingila Roy Hodgson, ya gayyaci dan wasan West Brom na gaba Saido Berahino a tawagar 'yan wasan kasar.

Hakan na nufin dan wasan mai shekaru 21 zai iya buga wa Ingila wasansa na farko, a karawar da za ta yi da Slovenia a Wembley ranar 15 ga watan Nuwamba, don neman cancantar shiga gasar kofin Turai na 2016.

Berahino, wanda aka haifa a Burundi, ya ci wa West Brom kwallaye bakwai, a wasanni goma na Premier a bana.

Hodgson, ya kuma gayyaci Micheal Carrick, da Stewart Downing da Theo Walcott a tawagar ta 'yan wasa 26 don karawar ta Slovenia da kuma wasan sada zumunta a Scotland ranar 18 ga watan Nuwamba.

Kocin na Ingila bai gayyaci dan wasan Liverpool Daniel Sturridge ba, saboda yana da rauni.