Bony zai sabunta kwantiragi da Swansea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ina da kyakkyawar dangantaka da 'yan wasa da ma'aikata da kuma magoya bayan Swansea

Dan wasan gaba na Ivory Coast Wilfried Bony, na gab da cimma yarjejeniyar sabon kwantiragi da kungiyar Swansea City.

A da ana rade-radin dan wasan mai shekaru 25 zai bar kungiyar a watan Yuli, bayan ya ci kwallaye 25 a shekararsa ta farko.

Swansea ta sayo shi kan fan miliyan 12 a 2012 kudin da ba ta taba kashewa wajen sayen dan wasa ba, kuma har yanzu yana da sauran shekaru uku a kwantiraginsa.

Dan wasan ya ce tattaunawa akan sabunta kwantiragin na tafiya daidai, kuma yana sa ran a kammala ta cikin makon nan.

Bony , ya ce, hankalinsa na kan Swansea kuma karin shekara daya a kwantiragin nasa abu ne da zai yi masa kyau.

Dan wasan ya ci kwallaye hudu a wasanni biyar na Swansea na baya bayan nan, bayan ya kasa ci a wasanninsu shida na farko na lig.

Ya ci wa Ivory Coast kwallaye biyu a gasar kofin duniya ta 2014, kuma rahotanni sun ce Arsenal da Liverpool da Tottenham na sha'awar sayen sa, amma kocin Swansea Garry Monk, ya ce ba na sayarwa ba ne.